Sanatan Kudu yace ba zai bari Shugaba Buhari ya tozarta a Majalisa ba

Sanatan Kudu yace ba zai bari Shugaba Buhari ya tozarta a Majalisa ba

- Sanatan Yankin Imo ya bayyana irin kokarin Gwamnatin Shugaba Buhari

- Dalilin haka yace sam ba za su bari Shugaba Buhari ya tozarta a Majalisa ba

- Sanatan na APC yace ‘Yan uwan sa ba su da karfin sake lokacin zaben 2019

Wani Sanatan Jihar Imo Benjamin Uwajomogu yace babu wanda ya isa ya kada Buhari a 2019. Sanatan yayi magana ne game da wani yunkuri da Majalisa ke yi. Sanatan yace yana ganin zai fi kyau Inyamurai su marawa Buhari baya har 2023.

Sanatan Kudu yace ba zai bari Shugaba Buhari ya tozarta a Majalisa ba

Babu wanda ya isa ya kada Buhari a 2019 inji wani Sanata

Sanatan da ke wakiltar Arewacin Jihar Imo Benjamin Uwajomogu ya bayyanawa manema labarai cewa yunkurin da ‘Yan uwan sa ke yi a Majalisar Tarayya na sauya tsarin gudanar da zaben 2019 ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.

KU KARANTA: Majalisa ta zargi wasu da hana ruwa gudu a harkar fetur

Sanata Benjamin Uwajomogu ya bayyana haka ne kwanan nan a babban birnin tarayya Abuja inda yace yunkurin da ‘Yan Majalisa ke yi bai da hurumi a doka don kuwa tsarin mulki bai ba kowa wannan dama ba illa Hukumar zabe na INEC.

‘Dan Majalisar dai yace za su goyi bayan Shugaba Buhari idan har ya soke kudirin da Majalisa tayi. Idan har mafi yawan ‘Yan Majalisa watau kaso 2/3 su ka amince da abin da Shugaban kasar yayi, shikenan ta zauna kuma babu yadda za ayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel