Buhari zai ci zabe a 2019 hankali kwance idan ya sake takara – Uzor Kalu

Buhari zai ci zabe a 2019 hankali kwance idan ya sake takara – Uzor Kalu

- Shugaba Buhari zai doke duk wanda ya tsaya takara inji Uzor Kalu

- Tsohon Gwamnan yace Talakawa za su zabi Shugaba Buhari a 2019

- Babban Jigon Jam’iyyar ya koka da barakar da ake samu a cikin APC

Tsohon Gwamnan Jihar Abiya ya fara neman goyon bayan mutanen Kasar Inyamurai da su ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya domin ya zarce a 2019 idan har ya sake neman takara. Kalu yace Buhari zai ci zabe sai dai in bai da lafiya.

Buhari zai ci zabe a 2019 hankali kwance idan ya sake takara – Uzor Kalu

Tsohon Gwamnan Abiya ya ce Talakawa za su zabi Buhari

Kamar yadda labari ya zo mana daga Jaridar Daily Trust, Uzor Kalu ya bayyana cewa ya kamata Jam’iyyar APC ta hada kai ta zama daya domin ta ci sunan ta na tsintsiya madauri guda. Tsohon Gwamnan ya koka da irin barakar da ke APC.

KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari yace sai an yi hakuri a Najeriya

Orji Uzor Kalu ya yabawa hangen nesan Shugaba Buhari da ya nada Bola Tinubu domin ya sasanta rikicin Jam’iyyar. A Jihohi da dama dai ana samun rikici tsakanin Ministan Gwamnatin Tarayya da Gwamnan Jihar musamman a Jihar Oyo.

Tsohon Gwamnan ya bayyana wannan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai kwanan nan a wani filin jirgi. A cewar tsohon Gwamnan na Abiya, kwanan nan Shugaba Buhari zai bayyana matsayar sa game da 2019 kuma zai lashe zaben.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel