Malami ya nemi gwamnatin tarayya ta dakatar da Shari’ar Diezani, Adoke, da wasu

Malami ya nemi gwamnatin tarayya ta dakatar da Shari’ar Diezani, Adoke, da wasu

Babban lauyan Najeriya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami ya bukaci shugaban kasa Buhari da ya dakatar da gwamnatinsa daga ci gaba da sauraron shari’ar tsohuwar ministar man fetur, Diezani Alison-Madueke da kuma tsohon akaunta janar na Najeriya, Bello Adoke bisa zarginsu da akeyi da hannu a badakalar Malabu.

A wata wasika da ya aika ga shugaban kasar, Malami ya ce binciken da gudanar akan shari’ar sun nuna masa cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ba ta da kwararan hujjoji akan mutane biyun da wasu da ake tuhuma.

Ya ce shari’ar za ta iya bayyana Najeriya ga sauran kasashen duniya a matsayin kasar da bai kamata a yarda da ita ba.

Malami ya nemi gwamnatin tarayya ta dakatar da Shari’ar Diezani, Adoke, da wasu

Malami ya nemi gwamnatin tarayya ta dakatar da Shari’ar Diezani, Adoke, da wasu

Idan dai bazaku manta ba, badakalar Malabu dai ta fara ne tun a shekarar 2011 a lokacin da gwamnatin Goodluck ta amince da sayar da Rijiyar man fetur ta OPL 245 daga hannun kamfanin Malabu zuwa hannun kamfanin Shell da Agip.

Diezani da Adoke na daga ciki wadanda suka yi yarjejeniya cinikayyar mai cike da alamun tambaya.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar matasan arewa ta roki Makarfi ya fito takarar shugaban kasa

A baya Legit.ng ta rahoto cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga dukkan yan Najeriya, musamman manyan shugabanni da su shirya sadaukar da abubuwa a matsayin ginshikin ci gaban kasa.

Ya ce a rayuwar kasa, akwai lokuta da ya zama dole yan kasa su manta da wani jin dadi ko kuma su sadaukar da wasu abubuwa domin ci gaba da hadin kan kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel