Labari da duminsa: Shugaba Buhari ya ja kunnen magu, ya bashi wa'adin kwana hudu ya kare kansa

Labari da duminsa: Shugaba Buhari ya ja kunnen magu, ya bashi wa'adin kwana hudu ya kare kansa

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da wata takardar jan kunne ga shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Ibrahim Magu

- Buhari ya bukaci Magu da ya aike da takardar kare kansa cikin kwanaki hudu kacal ga ministan shari'a

- Buhari ya aike wa Magu takarar jan kunnen bisa tuhumar da EFCC ke yiwa alkalin kotun da'ar ma'aikata, Danladi Yakubu Umar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da wata takardar jan kunne ga shugaban rikon kwarya na hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Ibarahim Magu.

A takardar jan kunnen mai lamba DPP/ADV:368/15 da jaridar Daily Post ta rawaito cewar ta samu daga PRNigeria, shugaba Buhari ya bukaci Magu da ya aike da takardar kare kansa zuwa ofishin ministan shari'a cikin kwanaki hudu kacal.

Labari da duminsa: Shugaba Buhari ya ja kunnen magu, ya bashi wa'adin kwan ahudu ya kare kansa

Ibrahim Magu

Shugaba Buhari ya aikewa Magu takardar ne ranar 16 ga wata, sannan ya bashi zuwa ranar 20 ga wata ya kare kansa bisa tuhumar da yake yiwa alkalin kotun da'ar ma'aikata, Danladi Yakubu Umar.

A cikin takardar da babban sakatare a ofishin shigar da kara na kasa, Mista Dayo Apata, ya saka wa hannu, shugaba Buhari ya bukaci Magu ya yi bayanin dalilin da ya saka shi tuhumar mai shari'a Danladi Yakubu Umar da laifin cin hanci bayan hukumar EFCC ta wanke shi a baya har sau biyu.

DUBA WANNAN: Jam’iyyar APC ta saukaka mana hanyoyin cin zaben 2019 – Makarfi

"Ina mai sanar da kai bukatar aika hujjojinka ga ofishin ministan shari'a a kan tuhumar alkalin kotun da'ar ma'aikata," kamar yadda yake a takardar.

Magu kan iya fada wa tsaka mai wuya bisa tuhumar da yake yiwa Danladi Umar musamman ganin cewar fadar shugaban kasa na zargin bai shawarci ofishin ministan shari'a ba kafin ya sake bude sabon babin tuhumar alkalin bayan a baya hukumar EFCC ta wanke shi daga dukkan zargin almundahana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel