Babban lauyan gwamnati ya shawarci Buhari ya dakatar da EFCC daga binciken tsohuwar minista Diezani Allison da Bello Adoke

Babban lauyan gwamnati ya shawarci Buhari ya dakatar da EFCC daga binciken tsohuwar minista Diezani Allison da Bello Adoke

Babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami ya aika ma shugaban kasa Muhammadu Buhari wata zungureriyar wasika inda a ciki yake bukatar Buhari da ya dakatar da binciken da ake yi ma kan tsofaffin ministoci guda biyu.

Ministocin sun hada da tsohuwar ministan mai Diezani Allison Madueke da kuma tsohon ministan shari’a Muhammad Bello Adoke, wadanda ake bincikensu game da badakalar siyar da rijiyan mai ta Malabu, mai lamba OPL 245.

KU KARANTA: Banza ta fadi: Hukumar DPR ta rabar da litan mai 40,000 ga al’ummar jihar Kaduna

Ita dai wannan badakala ta samo asali ne a shekarar 2011, lokacin da tsohon shugaban kasa Jonathan ya bada umarnin a siyar da rijiyar man ga kamfanin Shell da na Agip-Eni daga hannun kamfanin Mai da iskar gas ta Malabu, mallakin wani tsohon ministan mai Dan Atete.

Hakan ta sanya jami’an gwamnatin da suka jagoranci cinikin siyar da rijiyar man un hada da Bello Adoke da Diezani, mutane biyu da hukumar yaki da rashawa, EFCC ke ta dakon kamawa tun bayan kaddamar da bincike kan lamarin, amma sun tsere daga Najeriya.

Sai dai ana wata ga wata, kwatsam sai ga ministan shari’a Abubakar Malami ya aika ma Buhari wasika, inda yake cewa biciken da ya gudanar ya nuna cewar EFCC ba ta da wata madogara kwakkwara dake nuna Bello Adoke, Diezani Allison da sauransu sun tafka badakala.

Baya da haka, Malamai yace idan gwamnati ta cigaba da matsin lamba ga wadannan mutane, kasashen wajen ka iya kallon Najeriya a matsayin kasar da ba ta da alkibla, kuma wacce bata iya cika alkawurranta ga masu zuba hannun jari daga kasashen ketare.

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito baya ga ministan shari’a, shima karamin ministan mai, Ibe Kachikwu ya shawarci gwamnatin tarayya da ta kyale kamfanin Agip-Eni su cigaba da gudanar da ayyukansu akan rijiyan da ake hasashen tana dauke da gangan mai biliyan 9.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel