Jam’iyyar APC reshen Kaduna ta dakatar da El-Rufa’i na tsawon Watanni 6

Jam’iyyar APC reshen Kaduna ta dakatar da El-Rufa’i na tsawon Watanni 6

Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa wani sashi na jam’iyyar APC rashen jihar Kaduna ta dakatar da gwamnan jihar, Nasir El-Rufai har na tsawon watanni shida.

Hakan ya biyo bayan zargin sa da aikata abubuwan da suka saba ma jam’iyyar da na rashin imani.

Bangaren mai suna Kaduna Restoration group na karkashin shugabancin sanata Suleiman Hunkuyi.

Banda El-Rufa’i, bangaren ya kuma dakatar da masu taimaka masa guda uku na tsawon watanni 18.

Jam’iyyar APC reshen Kaduna ta dakatar da El-Rufa’i na tsawon Watanni 6

Jam’iyyar APC reshen Kaduna ta dakatar da El-Rufa’i na tsawon Watanni 6

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi 18 ga watan Fabrairu, bangaren ya bayyana cewa El-Rufa’i ya yi watsi da gayyatar da kwamitin gudanarwa na jam’iyyyar ya yi masa domin ya zo ya kare kan shi game da zargin da ake masa.

Sanarwa ta bayyana cewa sai da aka baiwa gwamnan wa’adin kwanaki 2 ya bayyana a gaban kwamitin, amma ya yi kunnen uwar shegu.

KU KARANTA KUMA: Hadimin gwamnan jihar Katsina ya kashe yarsa da mota

A don haka ne kwamitin gudanarwar a karkashin shugabancin S.I. Danladi Wada ya yanke hukuncin dakatar da shi a karkashin dokokin Jam’iyyar, bayan wata ganawa da jigajigan ta.

Sanarwar ta ce ganawar ta samu halartar ‘yan jam’iyyar APC na jahar, ‘yan majalisun Tarayya na jihar, mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga dukkan yan Najeriya, musamman manyan shugabanni da su shirya sadaukar da abubuwa a matsayin ginshikin ci gaban kasa.

Ya ce a rayuwar kasa, akwai lokuta da ya zama dole yan kasa su manta da wani jin dadi ko kuma su sadaukar da wasu abubuwa domin ci gaba da hadin kan kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel