Wasikar Obasanjo: Zamu mayar masa da martani nan bada dadewa ba – Dattawan jihar Katsina

Wasikar Obasanjo: Zamu mayar masa da martani nan bada dadewa ba – Dattawan jihar Katsina

Kungiyar dattawan jihar Katsina ta tabbatar da cewar zata mayar ma tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo raddi game da wasikar da ya aika ma Buhari nan bada dadewa ba.

Dattawan sun bayyana haka ne jim kadan bayan sun gada da shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidansa dake garin Daura na jihar Katsina, inda suka kai masa ziyara a karshen makon da ya gabata.

KU KARANTA: Banza ta fadi: Hukumar DPR ta rabar da litan mai 40,000 ga al’ummar jihar Kaduna

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari wanda ya jagoranci tawagar dattawan ya shaida ma manema labaeu cewa “Kungiyar mu zata duba yiwuwar yi ma Obasanjo raddi nan bada jimawa ba, zamu watsa raddin a manyan jaridun kasar nan.” Sai dai Masari bai bayyana ra’ayinsu game da wasikar ba.

Wasikar Obasanjo: Zamu mayar masa da martani nan bada dadewa ba – Dattawan jihar Katsina

Buhari tare da Dattawan jihar Katsina

Daga karshe Masari yace sun kai ma Buhari ziyarar ce don jajanta masa game da mutuwar yan uwansa mata guda biyu da ya rasa, Aisha Mamman da Halima Dauda.

“Muna fatan Allah ya jikansu, kuma Ya yi musu gafara, kuma mun fada ma Buhari ya dauki mutuwar a matsayin kaddara daga Allah.” Inji shi.

Wasikar Obasanjo: Zamu mayar masa da martani nan bada dadewa ba – Dattawan jihar Katsina

Dattawan jihar Katsina

Idan za’a tuna tsohon shugaban kasa Obasanjo ya shawarci shugaba Buhari da kada ya kuskura ya tsaya takara a 2019 saboda ya gaza a wajen cika alkawurran da ya daukan ma yan Najeriya a yayin yakin neman zabe.

Wasikar Obasanjo: Zamu mayar masa da martani nan bada dadewa ba – Dattawan jihar Katsina

Dattawan jihar Katsina

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel