Wasu mambobin jam’iyyar APC sun gudanar da zanga-zanga a ofishin jam’iyyar dake Abuja dan nuna rashin goyon bayan Oyegun

Wasu mambobin jam’iyyar APC sun gudanar da zanga-zanga a ofishin jam’iyyar dake Abuja dan nuna rashin goyon bayan Oyegun

- Wasu ‘ya’yan jam’iyyar APC sun gudanar da zanga-zanga a ofishin jam’iyyar dake Abuja

- Mambobin APC da suka gudanar da zanga-zanga ofishin jam’iyyar dake Abuja sun yi kira da Oyegun yayi murabus daga kan mukamin sa

Wasu ‘ya'yan jam’iyyar APC sun gudanar da zanga-zanga a ofishin jam’iyyar dake Abuja dan nuna rashin goyon bayan su ga shugaban jam’iyyar ya na kasa Cif John Oyegun.

Masu zanga-zangar suna kira ga, Cif John Oyegun, yayi murabus da kan mukamin sa na shugaban jami’iyyar APC na kasa.

Sun rubuta a kwalayen da suka rike yayin da suke gudanar da zanga-zangar cewa, cigaba kasancewar, Cif John Oyegun a matsayin shugaban jami’iyyar APC babban barazana ce ga cigaban jam’iyyar wasu kuma sun ce, yazama dole Oyegun yayi murabus.

Wasu mambobin jam’iyyar APC sun gudanar da zanga-zanga a ofishin jam’iyyar dake Abuja dan nuna rashin goyon bayan Oyegun

Wasu mambobin jam’iyyar APC sun gudanar da zanga-zanga a ofishin jam’iyyar dake Abuja dan nuna rashin goyon bayan Oyegun

Idan aka tuna baya Legit.ng ta rawaito muku labarin zanga-zangar da wasu ‘yan APC suka gudanar a ranar juma’a da ta gabata a sakatariyan jam’iyyar.

KU KARANTA : Makiyaya suna ci gaba da kai mana hari a jihar Benue - Gwamna Samuel Ortom

Wasu na ganin cewa tsohon gwamnan jihar Legas Bola Tinubu na da hannu a shirya wannan zanga-zanga ganin yadda suke zaman doya da manna shi Oyegun.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel