Kungiyar matasan arewa ta roki Makarfi ya fito takarar shugaban kasa

Kungiyar matasan arewa ta roki Makarfi ya fito takarar shugaban kasa

- Kungiyar matasan arewa (ACYD) ta roki Makarfi da ya shiga sahun masu zawarcin kujerar shugaban kasan Najeriya

- Shugaban kungiyar, Ibrahim Suleiman, ya sanar da haka ga manema labarai jiya a Kaduna

- Kungiyar ta bayyana cewar kwazon Makarfi lokacin yana gwamna ya saka take goyon bayansa

Wata kungiyar matasan Arewa (Arewa Concerned Youths and Development (ACYD)) ta roki tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi, da shiga cikin sahun masu neman shugabancin Najeriya a karkashin jam'iyyar PDP.

Shugaban kungiyar, Ibrahim Suleiman, ne ya yi wannan kira ga Makarfi a wata ganawa da ya yi da manema labarai jiya a Kaduna.

Kungiyar matasan arewa ta roki Makarfi ya fito takarar shugaban kasa

Ahmed Makarfi

Shugaban kungiyar ya ce dukkan shugabannin ta na jihohin arewacin Najeriya 19 sun amince da bukatar yin kira ga Makarfi ya fito neman shugabancin Najeriya a taron da kungiyar ta gudanar a Kaduna.

Suleiman ya ce sun ga cancantar Makarfi ne saboda irin kwazon da ya nuna lokacin yana gwamnan jihar Kaduna.

DUBA WANNAN: Jam’iyyar APC ta saukaka mana hanyoyin cin zaben 2019 – Makarfi

"Mun taru a nan ne domin tabbatar da goyon bayan mu ga Sanata Makarfi tare da rokon shi ya amsa wannan bukatar ta mu," a cewar Suleiman.

Suleiman ya kara da cewar Makarfi ya yi rawar gani lokacin yake gwamna a jihar Kaduna ta fuskar aiyukan raya kasa da hadin kan kabilun jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel