Ku shirya sadaukar da abubuwa domin ci gaban kasa – Buhari ga yan Najeriya

Ku shirya sadaukar da abubuwa domin ci gaban kasa – Buhari ga yan Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga dukkan yan Najeriya, musamman manyan shugabanni da su shirya sadaukar da abubuwa a matsayin ginshikin ci gaban kasa.

Ya ce a rayuwar kasa, akwai lokuta da ya zama dole yan kasa su manta da wani jin dadi ko kuma su sadaukar da wasu abubuwa domin ci gaba da hadin kan kasa.

A cewar wata sanarwa daga babban mai bashi shawara a kafofin watsa labarai, Garba Shehu, shugaban kasar yayi Magana a wajen wani taro da yayi a ranar Lahadi a Daura tare da manyan mazauna Katsina.

Yayinda yake yaba ma mambobin kungiyar kan yabama kokaroin gwamnatinsa wajen ci gaban kasa, shugaban kasar ya basu tabbacin cewa tsaron rayuka, dukiyoyin dukkan yan Najeriya zai ci gaba da samun kulawa na musamman.

Ku shirya sadaukar da abubuwa domin ci gaban kasa – Buhari ga yan Najeriya

Ku shirya sadaukar da abubuwa domin ci gaban kasa – Buhari ga yan Najeriya

A nashi jawabin, Masari yace tawagar sun je mahaifar shugaban kasar ne domin suyi masa ta’aziyya na rashin yan uwansa guda biyu.

KU KARANTA KUMA: Lamido ya tarbi masu sauya sheka zuwa PDP 5000 a Jigawa, ya sha alwashin kayar da Buhari a 2019

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wani abun bakin ciki ya faru a ranar Juma’a a jihar Katsina lokacin da mai ba Gwamna Aminu Masari shawarar na musamman akan al’amuran addini, Abdullahi Darma, ya take yarsa, A isha da mota bisa tsautsayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel