Labari da dumi-dumi: Yan Boko Haram sun far ma motocin haya a Borno, sun sace fasinjoji
1 - tsawon mintuna
Labarin da ke shigowa yanzu na nuna cewa yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram sun kai mumunan hari kan motocin hayan da soji ke rakawa a hanyar Maiduguri-Damboa misalin karfe 12 na ranan Asabar da ya gabata. Jaridar Sun ta samu rahoto.
Cikakken bayani kan wannan abu ya yi tsada saboda ko hukumar soji bata tabbatar da faruwan wannan ba, amma yau Litini, majiya ya bayyana cewa da yiwuwan anyo garkuwa da wasu fasonjojin motocin.
Wata majiya ta bayyana cewa lallai anyi garkuwa da mutane yayinda ake harbe-harbe.
Zaku tuna cewa an kulle hanyan Maiduguri-Damboa a watan Mayun 2014, amma babban hafsan soji, Laftanan Janar Tukur Buratai ya bude a Fabrairun 2016.
Asali: Legit.ng