Zubar da jini ya fi man fetur sauki a Najeriya – Shehu Sani

Zubar da jini ya fi man fetur sauki a Najeriya – Shehu Sani

- Shehu yace duk lokacin da kasa ta daina damuwa da balai’in dake afka mata, tabbas an cire tausayi a zukatan mutanen kasar

- Sanata Shehu Sani ya ce manyan 'yan siyasan Arewa sun kame baki su sun yi shiru akan kashe-kashen da ake yi a kasar saboda tsoron kada a kira su makiyan gwamnati tarayya

Shehu Sani, sanata mai wakilatr mazabar Kaduna ta tsakiya, yace zubar da jini ya fi man fetur sauki a Najeriya.

Sani yace Najeriya ta zama kasar da ake kashe-kashe da yin janaizar mutane da yawa a lokaci daya.

Sanatan yace duk lokacin da kasa ta daina damuwa da balai’in dake afka mata, tabbas an cire tausayi a zukatan mutanen kasar.

Zubar da jini ya fi man fetur sauki a Najeriya – Shehu Sani

Zubar da jini ya fi man fetur sauki a Najeriya – Shehu Sani

“ Zubar da jini ya fin man fetur sauki a Najeriyan mu ta yanzu. Babban bala’in da muke fuskanta a kasar nan shine kashe-kashe ya zama ruwan dare a rayuwan mu.

KU KARANTA : An kusa kashe ni saboda na ki barin kananan yara su kada zabe – Tsohon kwamishinan INEC

“Manyan ‘yan siyasan Arewa sun kame bakin su sunyi shiru saboda suna tsoron kada a musu kallon makiyan gwamnatin tarayya.

Sanatan yace Lokacin yayi da yakamata Buhari ya hana gwamnoni barin ayyukan dake gaban su dan kawo mishi ziyara.

Gwamnoni sun mayar da ziyarta shugban kasa Muhammadu Buhri al’ada, kusan kowani rana sai kaga gwamna ya bar aikin dake gaban sa dan kawo wa shugaban kasa ziyara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel