Yan hana ruwa gudu ke haddasa rashin man fetur a Najeriya – Kwamitin majalisar wakilai

Yan hana ruwa gudu ke haddasa rashin man fetur a Najeriya – Kwamitin majalisar wakilai

- An zargi yan hana ruwa gudu da haddasa karancin man fetur da ake fama da shi a fadin Najeriya

- Kwamitin binciken ayyukan ma’aikatan NPMC na majalisar wakilai ne ta bayyana hakan

- Shugaban kwamitin, Danlami Kurfi, ya bayyana cewa wadannan mutane suna buwayar kokarin gwamnatin tarayya

Majalisar wakilai ta zargi yan hana ruwa gudu da haddasa karancin man fetur a fadin kasar.

Kwamitin binciken ayyukan ma’aikatan NPMC na majalisar wakilai ne ta bayyana hakan a ranar Alhamis, 15 ga watan Fabrairu.

A lokacin da ya kai wani ziyara matatar Port Harcourt, shugaban kwamitin, Danlami Kurfi ya ce wadannan yan hana ruwa sune suka hadda karancin man fetur da ake fuskanta a kasar.

Yan hana ruwa gudu ke haddasa rashin man fetur a Najeriya – Kwamitin majalisar wakilai

Yan hana ruwa gudu ke haddasa rashin man fetur a Najeriya – Kwamitin majalisar wakilai

Kurfi wanda ya kasance dan majalisa mai wakiltan Dutsin-ma/Kurfi na jihar Katsina, yace binciken da kwamitin tayi zuwa yanzu ya nuna cewa gwamnati a bangarenta ta NNPC tana samar da lokaci domin shawo kan matsalar.

KU KARANTA KUMA: Hadimin gwamnan jihar Katsina ya kashe yarsa da mota

Dan majalisar ya bayyana cewa wasu ne ke buwayar kokarin da gwamnati ke yi.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Alhaji Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa sannan kuma dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar PDP yayinda yake tarban sama da mutane 5,000 da suka sauya sheka daga APC zuwa PDP ya sha alwashin kayar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019 idan har jam'iyyarsa ta basa tikitin takarar shugabancin kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel