An kusa kashe ni saboda na ki barin kananan yara su kada zabe – Tsohon kwamishinan INEC

An kusa kashe ni saboda na ki barin kananan yara su kada zabe – Tsohon kwamishinan INEC

- Ferfese Olurude ya ce da kyar ya sha da ransa a wani yankin kasar nan saboda ya hana kananan yara kada kuri'a

- Olurude yayi kira da gwamnatin APC ta gudanar da zaben da ya fi na shekara 2015 inganci

Wani tsohon kwamishinan hukumar gudanar da zabe mai zaman Kanta (INEC), Ferfesa Lai Olurode, ya ce sai da aka kusan kashe shi a wani yankin kasar nan saboda yaki barin kanana yara su kada zabe a shekarun baya da suka gabata.

Yayi kira da gwamnatin tarayya ta tabatar da an ba ma’aikatan gudanar da zabe kariya a kasar nan wanda mafi akasarin su masu bautan kasa ne.

Ferfesa Olorude, yayi kwamishinan hukumar INEC reshen gudu maso yamma daga shekara 2010 zuwa 2015.

An kusa kashe ni saboda na ki barin kananan yara su kada zabe – Tsohon kwamishinan INEC

An kusa kashe ni saboda na ki barin kananan yara su kada zabe – Tsohon kwamishinan INEC

Olurode ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da manema labaru a ranar Lahadi a lokacin da yake mayar da martani akan rahotannin da suka nuna kananan yara suna cikin wadanda suka kada zabe, a zaben kanan hukumomin da aka gudanar a makon da ta gabata a Kano.

KU KARANTA : Kungiyar IPMAN ta bayyana yadda zai a iya kawo karshen karancin man fetur a Najeriya

Kwamishinan yace, idan aka wayar da kawunan mutaen yankin akan illar barin kananan yara suka kada zabe al’amarin zai ragu.

“Da kyar na sha da raina a wani cibiyan zabe na wani banagren kasar nan ,saboda mutanen wurin sun ce dole sai an bar kananan yara sun kada zabe ko kuma babu zabe a yankin.

Gwamnatin APC tana da aiki babba a gabanta, ya zama dole ta tabbatar da a gudanar da zaben da zai fi na shekara 2015 ingaci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel