Obasanjo ya yi amai ya lashe: Ya yabawa kokarin gwamnatin Buhari

Obasanjo ya yi amai ya lashe: Ya yabawa kokarin gwamnatin Buhari

A wani abu mai kama da tufka da warwara, tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, a karshen mako da ya gabata ya jinjinawa shugaba Muhammadu Buhari kan samun nasara a wuraren da gwamnatocin da suka gabata suka fadi.

Yayinda tsohon shugaban kasan ke magana a taron kaddamar da gina matatan man Azikiel, matata mai zaman kanta na farko a yankin Neja Delta, ya jinjinawa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari kan kokarin bada lasisin gina matatai 22 a fadin kasa.

Ya bayyana cewa gwamnatinsa da ta shude ta bada lasisi 18 amma bata iya kaddamar da ginawa ba.

Obasanjo ya yi amai ya lashe: Ya yabawa kokarin gwamnatin Buhari

Obasanjo ya yi amai ya lashe: Ya yabawa kokarin gwamnatin Buhari
Source: Twitter

Yace: “An fada min cewa shugaba Buhari da gwamnatinsa sun bada lasisi 22 kuma kamfanin Azikiel kadai ce ta fara aiki a kai, kafin yanzu mun bada lasisi 18 amma babu wanda ya zantar”

“Sai koke-koke su keyi, wanda ya kunshi rashin tsaro da kudin mai. Amma har yanzu akwai wadannan koke-koke. Kawai dama suna son lasisi ne domin karban danyan mai.”

KU KARANTA: Kirkirar 'yan sandan jiha zai kara Dagula lamuran tsaro a kasar nan - Tsohon kwamishinan 'yan sanda

Zaku tuna cewa a watan jiya, tsohon shugaba Obasanjo ya rubuta wasika da ya girgiza kasa na cewa kada shugaba Muhammadu Buhari ya sake takara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel