Kirkirar 'yan sandan jiha zai kara Dagula lamuran tsaro a kasar nan - Tsohon kwamishinan 'yan sanda

Kirkirar 'yan sandan jiha zai kara Dagula lamuran tsaro a kasar nan - Tsohon kwamishinan 'yan sanda

- Tsohon kwamishinan 'yan sandan Najeriya a jihar Legas, Abubakar Tsav, ya ce har yanzu Najeriya ba ta kai munzalin kirkirar 'yan sandan jiha ba

- Tsav ya ce kirkirar 'yan sandan jiha a halin yanzu zai kara dagula lamarin tsaro a kasar nan

- Ya ce gwamnonin dake amfani da jami'an 'yan sanda a yanzu zasu yi amfani da 'yan sandan jiha yadda ransu ke so

Tsohon kwamishinan 'yan sandan a jihar Legas, Abubakar Tsav, ya ce har yanzu Najeriya bata kai munzalin kirkirar 'yan sandan jiha ba kamar yadda wasu ke bijiro da bukatar yin hakan ba.

Tsav na wannan kalamai ne yayin a wani jawabi da ya aike wa wakilin jaridar Punch a jiya, Lahadi.

Kirkirar 'yan sandan jiha zai kara Dagula lamuran tsaro a kasar nan - Tsohon kwamishinan 'yan sanda

Tsohon kwamishinan 'yan sanda, Abubakar Tsav

"Kirkirar 'yan sandan jiha zai bayar da wata kafa da zata kawo durkushewar Najeriya cikin sauri," a cewar Tsav.

Tsav ya ci gaba da cewa "ko a halin yanzu gwamnoni basa iya kulawa da jami'an 'yan sanda dake aiki a jihohin su, sannan za su yi amfani da 'yan sandan jiha domin biyan bukatun kansu."

DUBA WANNAN: Hukumar JAMB ta tsayar da ranar yin jarrabawar gwaji ga daliban da suka yi rijista

Tsav ya ce 'yan siyasa ne babban tarnaki ga kirkirar 'yan sandan jiha a Najeriya domin zasu mayar da harkar tsaro ta koma siyasa, su dasa wanda suke so, su tsige wanda basa so, hakan kuma ba zai haifar da da mai ido ba a bangaren tsaro.

Tsav ya bukaci masu kiraye-kirayen a kafa 'yan sandan jiha da su dakata tukunna har sai Najeriya ta kara hankali.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel