Kungiyar Boko Haram: Wata kotun Najeriya ta wanke mutane 475 daga zargi

Kungiyar Boko Haram: Wata kotun Najeriya ta wanke mutane 475 daga zargi

Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu, wata kotu a Najeriya ta saki mutune akalla 475 da gwamnatin kasar a baya ta ke zargin su da kasancewa mambobin kungiyar nan ta ta'addanci ta Boko Haram bayan da aka gano ba su da alaka kai tsaye da kungiyar.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin ministan shari'ar kasar kuma babban Antoni Janar watau Abubakar Malami, ya fitar inda ta ce kotun da ke yin shari'a ga mutanen da ake zargi da shiga Boko Haram wacce ke zamanta a garin Kainji na jihar Naija ce ta yanke hukuncin.

Kungiyar Boko Haram: Wata kotun Najeriya ta wanke mutane 475 daga zargi

Kungiyar Boko Haram: Wata kotun Najeriya ta wanke mutane 475 daga zargi

KU KARANTA: Dan jihar Katsina ya jawowa Najeriya abun alfahari

Legit.ng ta samu haka zalika cewa sanarwar har ila yau ta bayyana cewa kotun ta sallami mutanen ne a ranar Juma'a da ta gabata bayan wani zaman kotun da ta gudanar a sirrance.

A wani labarin kuma, Akalla mutane uku suka sha harsashen bindigar jami'an 'yan sandan nan na Najeriya ya runduna ta musamman dake yaki da fashi da makami watau Special Anti-Robbery Squad, SARS shiyyar jihar Plateau, garin Jos a wata mashayar jiya.

Lamarin dai kamar yadda muka samu daga majiyoyin sun tabbatar da cewa ya faru ne a ranar Litinin din da ta gabata kuma wadanda aka harba din sun hada da Dung Chung, dan shekaru 42 dake sana'ar kafinta.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel