Bukola Saraki na gayyatar Emmanuella mai barkwanci majalisa, domin su taimaka mata

Bukola Saraki na gayyatar Emmanuella mai barkwanci majalisa, domin su taimaka mata

- Akalla mutum miliyan ke kallon tashar ta a Youtube

- An gayyaceta Amurka domin a sanya ta a fim

- Shima Bukola Saraki ya gayyaceta majalisa

Bukola Saraki na gayyatar Emmanuella mai barkwanci majalisa, domin su taimaka mata

Bukola Saraki na gayyatar Emmanuella mai barkwanci majalisa, domin su taimaka mata

Emanuella, ja'irar yarinya mai barkwanci a bidiyo, ta sake samun tagomashi, tun bayan da tasharta ta bidiyon youtube ta hada masu bibiya mutum miliyan guda, sai kara sama-sama take yi inda ta zama hamshakiyar mai kudi.

Yanzu dai shugaban Majalisar Dattijai, na ukku a kasar nan, ya gayyaceta majalisar a duk ranar da ta iso Najeriya domin su duba yadda zasu taimaka mata da ma sauran yara masu kwakwalwa kamarta.

A sakonsa ta tuwita, dattijoon ya taya ta murna da gayyatar da kamfanin fina-finan Hollywood wato Disney World, suka yi mata domin ta fara fitowa a fina-finansu.

DUBA WANNAN: Almajirai sun taka a kafa daga Katsina zuwa Bauchi

Sarakin, bayan taya ta murna, ya kuma ce taje da ikon Allah, kuma yana mata fatan zata baiwa duniya dariya kamar yadda a shekarun nan take yi ga 'yan Najeriya.

Duniya dai na fara kallon kasar nan a matsayin kasa mai kima, da kwakwalwa, tun bayan da muka yi zarra a fannin tattalin arziki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel