Nigerian news All categories All tags
Ana takaddama kan shirin rushe kananan hukumomi da ake yi a Najeriya

Ana takaddama kan shirin rushe kananan hukumomi da ake yi a Najeriya

- Ana ta cigaba da muhawara kan shirin rushe kananan hukumomi a Najeriya

- An kafa kwamiti karkashin jagorancin Gwamna Nasir El-Rufai

- Kungiyoyi da dama suna ganin hakan bai kamata ba

Ana takaddama kan shirin rushe kananan hukumomi da ake yi a Najeriya

Ana takaddama kan shirin rushe kananan hukumomi da ake yi a Najeriya

Wani sabon babi da aka bude dangane da makomar kananan hukumomi a Najeriya, ya haifar da sabuwar muhawara a tsakanin masu ruwa da tsaki a kasar da ma jama'ar kasar.

Kwamitin da Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta nada a karkashin Gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufa'I, domin ya kago hanyar da za a bi wajen gyaran fasalin kasar, ya mika rahoto inda ya ba da shawarar a rushe kananan hukumomi.

Wannan shawara ta gamu da fushin kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi ta NULGE da ma wasu ‘yan kasa.

DUBA WANNAN: Wata Sabuwa: An kama wani ma'aikacin JAMB da badakalar miliyoyin nairori

Shi dai rahoton ya ba da shawarar cewa a ruguje kananan hukumomin a hade muhimman ayyukan da suke yi da jihohi.

Sai dai tuni, wannan rahoto ya fara shan suka daga masu ruwa da tsaki a wannan fanni.

“Kwanan nan ake dawo da mutane daga Libya, sun je an mayar da su bayi, idan kananan hukumominsu suna aiki yadda ya kamata, wallahi babu matashin da zai bar kauyansu ya tafi Libya.” Inji Shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta NULGE a Najeriya, Ibrahim Khalil.

Sai dai yayin da ake wannan takaddama, wasu na ganin bai wa kananan hukumomin ‘yancin cin gashi kansu shi ne mafita.

“Sai an ba kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kansu, talaka ne ya zabi gwamnatin nan…. Ba fa mulkin soja mu ke yi ba.” Inji Nasiru Kabir, na kungiyar matasa ta Nigerian Youths for Positive Change da ke fafatukar neman sauyi na gari.

Sai dai dan majalisar wakilai, Muhamamd Musa Soba, ya ce, wannan batu na rushe kananan hukumomi shawara ce kawai kwamitin ya bayar.

“Wannan shawara ce kwamitin ya bayar, ba wai matsaya ba ce ta jam’iyar APC, ita kanta jam’iyyar sai ta zauna ta duba ta ga me ya kamata a yi.” A cewar Soba.

Batun kananan hukumomi a Najeriya, lamari ne da ke janyo zazzafar muhawara, domin kananan hukumomin, su ne rassan gwamnati mafi kusa da jama'ar kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel