Nigerian news All categories All tags
Dubun wasu 'yan fashi da su ka addabi Sakkwato ta cika

Dubun wasu 'yan fashi da su ka addabi Sakkwato ta cika

- 'Yansanda sun kama wasu 'yan fashi 5 da su ka addabi Sokoto na tsawon shekaru 5

- Mai magana da yawun Hukumar 'Yansanda na Jihar, ASP Cordelia Nwewe, ita ce ta bayyana hakan

- Ta kuma ce an kama wadansu ma su safaran kwayoyi su 2 da katan-katan na kodin

'Yansandan Jihar Sokoto sun kama wasu 'yan fashi da a ke zargi da addaban Jihar da fashi da makami na tsawon shekaru 5. Hukumar ta kuma kama wasu ma su safaran kwayoyi da katan katan na kodin.

Dubun wasu 'yan fashi da su ka addabi Sokoto ta cika

Dubun wasu 'yan fashi da su ka addabi Sokoto ta cika

Mai magana da yawun Hukumar 'Yansanda, ASP Cordelia Nwewe, ta bayyana cewar wani mai suna Ali Abubakar na Karamar Hukumar Yabo da wasu mutane 4 da wani Ahmad Abubakar na Jihar Kwara, sun addabi mutanen Kauyen Sakewa na Karamar Hukumar Bodinga da fashi da makami.

KU KARANTA: NAFDAC ta garkame gidajen gasa mummuki guda 24 a Borno

Ta ce sun amsa laifin na su ne yayin da a ke tuhumar su. Sun kuma bayyana cewar wani Nafi'u Umar, wanda shi ma an kama shi, shi ne ya ba su umurnin yi wa makocin sa fashi. An kama su da muggan bindigogi, a na kuma kokarin kamo sauran mutane 3 daga cikin su.

Hakazalika an kama wani Abubakar Muhammad na Kauyen Baza da Ali Usman da Aliyu Abubakar na Kauyen Sauro, wadanda su ka raunata kuma suka kwace N300,000 da babur na N250,000 a hannun wani Abubakar Umar na Kauyen Kurjinga da ke Karamar Hukumar Yabo, 'Yan fashin sun kuma fyade matar sa.

Sai dai kuma Nwewe ta ce ba a samu damar kama abokan fashin na su ba tukunna, Kiruwa Sahabi da Abubakar ND Jabbi na Jihar Kebbi. A na nan dai a na neman su ruwa a jallo. Nwewe ta kuma ce an kama wasu ma su safaran kwayoyi su 2, wadanda za a gurfanar da su gaban shari'a idan bincike ya kammala.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel