Nigerian news All categories All tags
Muna da isashshen sarari ga duk masu son dawowa jam'iyyar mu - PDP

Muna da isashshen sarari ga duk masu son dawowa jam'iyyar mu - PDP

- Jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewar tana maraba ga 'ya'yan jam'iyyar dake da bukatar dawowa

- Sakataren yada labaran jam'iyyar, Kola Ologbondiyan, ya sanar da hakan ga manema labarai jiya a Abuja

- Ya ce jam'iyyar PDP a shirye take ta karbi masu son shigar ta a dukkan matakai

Jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewar a shirye take ta karba duk mai son dawowa cikinta tare da bayar da tabbacin cewar tana da isashshen sarari ga duk 'ya'yan ta.

Wannan na kunshe cikin wata takardar sanarwa da sakataren yada labaran jam'iyyar, Kola Ologbondiyan, ya fitar jiya a Abuja.

Muna da isashshen sarari ga duk masu son dawowa jam'iyyar mu - PDP

Sakataren watsa labaran PDP; Kola Ologbondiyan

Sanarwar ta ce, "kamar yadda sunan jam'iyyar mu ya nuna cewar ta jama'a ce, ina so na tabbatar wa 'yan Najeriya cewar muna maraba da duk dan kasa dake son shigowa jam'iyyar mu. Muna da wurin kowa da kowa."

DUBA WANNAN: Rade-radin komawar Saraki PDP: Matasa sun yi zanga-zangar nuna adawa

Jawabin ya kara da cewa, yanzu jam'iyyar PDP ta yi kyakykyawan tsarin siyasar cikin gida da zai bawa kowa dama ya taka rawar sa a siyasance musamman a bangaren fitar da 'yan takara da zasu wakilci jam'iyyar PDP a zabuka.

Jam'iyyar PDP ta bukaci 'yan Najeriya da su tashi domin hada karfi da ita wajen kawo karshen mulkin jam'iyyar APC da ta ce ya haifar da bakar wahala ga mutanen Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel