Nigerian news All categories All tags
Majalisar Wakilai ta fadawa Shugaban kasa Buhari bai isa ya saida kadarori ba

Majalisar Wakilai ta fadawa Shugaban kasa Buhari bai isa ya saida kadarori ba

- Yakubu Dogara yace ba za su bari a saida kadarorin kasar nan ba

- Shugaban Majalisar ya nemi a nemi kudi a tada kamfanin Ajaokuta

- Sama da mutane 10000 za su samu aikin yi idan aka gyara kamfanin

Mun samu labari cewa Shugaban Majalisar Wakilan Tarayya watau Rt. Hon. Yakubu Dogara ya fadawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa bai isa ya saida kadarorin kasar da ake ji da su ba.

Majalisar Wakilai ta fadawa Shugaban kasa Buhari bai isa ya saida kadarori ba

Dogara yace bai za a saida kadarorin Najeriya ba

Yakubu Dogara ya bayyana cewa kamfanin kera karafuna da ke Garin Ajaokuta a Jihar Kogi kadai ya isa ya canza kasar nan. A cewar Shugaban Majalisar Kasar, babu dalilin da zai sa ace wannan katafaren kamfani ya gaza aiki a kasar nan.

KU KARANTA: An kama wasu manyan barayi da su fitini jama'a a Najeriya

Majalisa dai ta bayyana cewa ba za ta zura idanu ta kuma kyale Gwamnatin Tarayya ta saida kadarorin kasar ba domin neman kudi. Yakubu Dogara yace sai dai za su marawa Shugaban kasar baya wajen ganin an babbako da kamfanin Ajaokuta.

Yakubu Dogara ya koka da yadda aka bari Kamfanin na Ajaokuta ya mutu inda ya kuma daura laifin kan Gwamnatocin baya. Idan an tada wannan kamfani, sama da mutane 10, 000 za su samu aiki amma ana bukatar kudi sama da Dala Miliyan 500.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel