Nigerian news All categories All tags
Barka: Likitoci sun samu nasarar raba wasu jarirai da aka haifa manne da juna a Bauchi

Barka: Likitoci sun samu nasarar raba wasu jarirai da aka haifa manne da juna a Bauchi

- Kwararrun likitoci sun samu nasarar raba wasu jarirai da aka haife su a manne da juna

- Sai dai guda cikin jariran bai kai labari ba, inda ya rasu jim kadan

Kwararrun likitoci a jihar Bauchi sun samu nasarar raba wasu jarirai yan biyu da aka haife su a manne da juna, kamar yadda gidan jaridar Birtaniya, BBC Hausa ta ruwaito.

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito guda cikin jariran bai kai labari ba, inda ya rasu jim kadan bayan an kammala aikin raba su, wanda wasu likitoci guda bakwai suka gudanar cikin sa’o’I biyu.

KU KARANTA: Najeriya da kasar Koriya ta Arewa zasu kulla sabuwar alaka don tabbatar da tsaro da zaman lafiya

Su dai wadannan jarirai an haifesu ne a watan Disambar da ta gabata, ga wata matashiya mai shekaru 20 a jihar Bauchi, sai dai ko a wancan lokacin, guda cikin jariran baya ya numfashi, wanda hakan ne ya sabbaba bukatar rabe su daga jikin juna.

Barka: Likitoci sun samu nasarar raba wasu jarirai da aka haifa manne da juna a Bauchi

Aikin

Da wannan dalili ne Kaakakin majalisar wakilai, Honorabul Yakubu Dogara ya dauki nauyin kudin tiyatan, amma majiyar ta kara da cewa ita kuwa dayar jaririyar ta rayu, kuma tana samun sauki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel