Nigerian news All categories All tags
Uwar bari: Shugaba Zuma ya amince zai yi murabus cikin watanni 3 zuwa 6

Uwar bari: Shugaba Zuma ya amince zai yi murabus cikin watanni 3 zuwa 6

Shugaban kasa Afrika ta kudu, Jacob Zuma, a yau Talata ya amince zai sauka daa karagar mulkin kasar cikin watanni uku zuwa shida.

Sakataren jam’iyyar ANC, Ace Magashule ya bayyana hakan ne yayin hira da manema labarai akan sakamakon ganawar shugabannin jam’iyyar da aka yi.

An yanke wannan shawara ne bayan zaman sa’o;i 13 ana kace-nace tsakanin Zuma da mataimakinsa, Cyril Ramaphosa.

An dade ana son cire shugaba Jacob Zuma amma abun ya gagara. A watan Disamban 2017, Ramaphosa ya kayar da wacce Zuma ke goyon baya a zaben shugabancin jam’iyyar.

Uwar bari: Shugaba Zuma ya amince zai yi murabus cikin watanni 3 zuwa 6

Uwar bari: Shugaba Zuma ya amince zai yi murabus cikin watanni 3 zuwa 6

Kuma a al’adan jam’iyyar, shugaba ne aka mikawa ragamar mulkin kasar. Da Zuma ya ji uwar bari ya amince daga karshe cew zai sauka daga mulkin shugabancin kasan.

Legit.ng ta kawo muku cewa Jam’iyyar ANC dake kan mulki a kasar Afrika ta Kudu ta bai wa shugaban kasa, Jacob Zuma wa’adin kwani biyu yayi murabus ko a tsige shi a lokacin da aka gaza samun matsaya a tattaunawar da akayi da shi da ya kwashe tsawon lokaci.

KU KARANTA: Shugaba Jacob Zuma na cikin tsaka mai wuya

Rahotannin da aka samu daga Kafofin watsa labaru na kasar Afrika ta kudu, sun nuna cewa jam’iyyar ANC za ta aike wa Shugaba Jacob Zuma wasikar sauka daga karagar mulkin kasar bayan ta yi watsi da alfarman da ya nema daga jam’iyyar na cewa a barshi akan mukamin sa na tsawon wasu ‘yan watanni.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa Da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel