Nigerian news All categories All tags
Da dumi-dumi: Rundunar sojin Najeriya sun fitittiki yan Boko Haram a Sabil Huda, sun ceto mata da yara

Da dumi-dumi: Rundunar sojin Najeriya sun fitittiki yan Boko Haram a Sabil Huda, sun ceto mata da yara

A jiya Litinin, Rundunar sojin Operation Lafiya Dole sun fitittiki yan tada kayar bayan Boko Haram a mabuyarsu na dajin Sambisa. Jami’an sun kara da ceto mata 19 da yara 27 daga hannun yan ta’addan.

Mun samu wannan labari ne a sanarwan mataimakin kakakin runduar Operation Lafiya Dole, Colonel Onyeama Nwachukwu inda yace:

“Rundunar sun fitittikesu daga daya daga cikin manyan mabuyarsa na cikin dajin Sambisa kusa da Sabil Huda.”

Da dumi-dumi: Rundunar sojin Najeriya sun fitittiki yan Boko Haram a Sabil Huda, sun ceto mata da yara

Da dumi-dumi: Rundunar sojin Najeriya sun fitittiki yan Boko Haram a Sabil Huda, sun ceto mata da yara

Ya kara da cewa an kai wannan gagarumin hari ne da taimakon jami’an sojin sama inda suka kama manyan makamai da ya kunsa Spartan Armoured Personnel Carriers (APC) guda 2, babban mota 1 da na’urar Komfuta 1.

KU KARANTA: Shehu Sani ya bayar da mafita

A karshe kuma rundunar sunyi kaca-kace da gidajen da suka gina a wajajen.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel