Nigerian news All categories All tags
Mahara yan bindige sun hallaka wani jami’in Dansanda, sun jefar da gawarsa

Mahara yan bindige sun hallaka wani jami’in Dansanda, sun jefar da gawarsa

Rundunar Yansandan jihar Nassarawa ta sanar da gano gawar wani jami’inta da aka yi ma kisan gilla, a kauyen Audu dake cikin karamar hukumar Obo na jihar Nassarawa, inji rahoton Channels TV.

Kaakakin rundunar, Idrissu Kennedy ne ya tabbatar da haka ga majiyar Legit.ng, inda yace dansanda na daga cikin tawagar Yansanda da rundunar ta aika domin kwantar da tarzoma a yankin kudancin jihar.

KU KARANTA: Kaico! An gano gawar wani Dansanda a jihar Benuwe, wanda yayi ɓatan dabo

Sauran jama’a dake yankin da lamarin ya farusun ranta ana kare, suka bar gidajensu, duk a sanadiyyar maharan, wanda ake zargin makiyaya ne, dake kai musu farmaki, musamman a cikin dare, lokacin da kowa ke barci.

Kaakaki Kennedy yace: “Yan bindigan sun harbi jami’in ne a lokacin da sauran abokan aikinsa suka yi kokarin mayar da wuta daga wajen maharban, kokarinsu su babbaka gidajen kauyen gaba daya. Amma ya tabbatar da sun kaddamar da bincike kan lamarin.

An samu karuwar ayyukan yan bindiga a yan kwanakin nan, musamman a jihohin Benuwe da Nassarawa, da kuma Taraba, don kuwa ko a jiya, sai da aka samo rahoton gani gawar wani dansansa a jihar Benuwe babu ido.

Haka zalika an bindige wasu jami’an hukumar tsaro ta farin kaya a wani kauyen Kasseyo dake cikin karamar hukumar Guma na jihar Benuwe.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel