Nigerian news All categories All tags
Jami'an tsaron NSCDC sun cafke 'yan ta'adda a jihohin Borno da Jigawa

Jami'an tsaron NSCDC sun cafke 'yan ta'adda a jihohin Borno da Jigawa

- Hukumar tsaro ta NSCDC ta damke wasu mutane hudu dake da barnar kayan wutar lantarki a Jigawa

- A Jihar Borno, hukumar tsaron NSCDC ta cafke wasu mutane bakwai dake tayar da hankula al'umma a wasu kauyuka

- Hukumar ta jaddada aniyar ta na yaki da masu barnatar da kayan gwamnati da aiyukan ta'addanci

Hukumar tsaro ta NSCDC ta yi nasarar damke wasu mutane hudu dake da hannu a satar wayar wutar lantarki a karamar hukumar Babura dake jihar Jigawa.

Wadanda aka kama din mazauna garin Gidan-Igiya ne dake karamar hukumar Dambatta a jihar Kano kuma an kama su ne yayin da suke kokarin tserewa da damin wayoyin da suka sata a cikin wata mota kirar Golf mai lamba AG 844 DBT.

Jami'an tsaron NSCDC sun cafke 'yan ta'adda a jihohin Borno da Jigawa

Jami'an tsaron NSCDC sun cafke 'yan ta'adda a jihohin Borno da Jigawa

Kakakin hukumar a jihar Jigawa, DSC Adamu Shehu, ya ce hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS) ce ta fara kama masu laifin kafin daga bisani su damka su hannun hukumar a jiya, Litinin.

A wani labarin mai kama da wannan, hukumar tsaro ta NSCDC ta kama wasu mutane bakwai dake tayar da hankalin jama'a a wasu kauyukan jihar Borno kamar yadda kwamandan hukumar, Mista Ibrahim Abdullahi, ya sanar a ganawar sa da manema labarai yau a Maiduguri.

DUBA WANNAN: Shugabannin hukumomin tsaron Najeriya sun yi gumm da bakinsu bayan ganawa da Buhari

Abdullahi ya ce, biyu daga cikin mutanen bakwai 'yan sintiri ne suka kama su yayin da ragowar mutane biyar an kama su a wani aiki da hukumar ta yi tare da 'yan kungiyar tsaro ta sa-kai.

Ya kara da cewar wadanda aka kama din na amfani da bindigar baushe tare da fakewa da cewar su 'yan Kungiyar Boko Haram ne, su na kwace shanun makiyaya da satar kayan jama'a.

Wadanda aka kama din sun amsa laifinsu da bakinsu, a cewar kwamanda Abdullahi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel