Nigerian news All categories All tags
Yaki da rashawa: Kotu ta sanya ranaku uku a jere don fara shari’ar Ibrahim Shema

Yaki da rashawa: Kotu ta sanya ranaku uku a jere don fara shari’ar Ibrahim Shema

Mai shari’a Mai Kaita Bako na babbar Kotun jihar Katsina, ya sanya ranakun 10, 22, da 12 na watan Afrilun bana a matsayin ranakun sauraron karar da hukumar EFCC ta maka Ibrahim Shehu Shema.

Mai shari’an ya bayyana haka ne a yayin zaman da ya gudana, bayan da Kotun daukaka kara ta jihar Kaduna ta fatattako Shema ya koma gaban Kotun ta katsina don ta saurari karar da aka shigar da shi, saboda a fari ya kalubalanci Kotun, wai bata da hurumin sauraron karar.

KU KARANTA: Kayyasa! Wata Mace ta lashe kyautar da ta gagari Jonathan da sauran shuwagabannin kasashen nahiyar AfirkaX

Channels TV ta ruwaito Shema ya shaida ma Kotun cewar ba’a takardun tuhume tuhumen da ake yi masa ba, kwatsam sai aka maka shi Kotu, inda Kotun ta ce masa yana da hurumin a bashi takardun nan a gaskiya, sai dai ta kara da cewa lokacin bada takardun bai yi ba tukunna.

Yaki da rashawa: Kotu ta sanya ranaku uku a jere don fara shari’ar Ibrahim Shema

Shema

Ana tuhumar tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema ne tare da wasu mutane guda uku, Sani Hamisu Makana, Lawal Ahmad Safana da Ibrahim Lawal Dankaba kan zargin cin amana, wulakanta ofishinsu da satar kudi naira biliyan 11.

Idan za’a tuna, a watan Satumbar 2016 ne hukumar EFCC ta shiga neman Shema ruwa a jallo, sakamakon zarginsa ta tafka satar naira biliyan 76, kuma duk kokain da ta yin a ganinsa ya ci tura.

Yaki da rashawa: Kotu ta sanya ranaku uku a jere don fara shari’ar Ibrahim Shema

Shema

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel