Nigerian news All categories All tags
Kotu ta daure mutane biyu da su ka yi sata a coci

Kotu ta daure mutane biyu da su ka yi sata a coci

- Samari 2 ma su shekaru 24 sun sace wayoyi 7 a coci

- Kotu ta yankewa kowannen su zaman gidan yari ma watanni 6

- Wannan lamari ya faru ne a Utako na garin Abuja

A yau Talata ne wata kotu a Garmo na garin Abuja ta yankewa wadansu barayi 2, zaman gidan yari na watanni 6 ga kowannen su. Barayin ma su sunaye Richard Christian da Komolafe Segun, sun sace wayoyin hannu 7 ne a coci.

Wasu maza 2 zasu bakunci gidan yari na watanni 6 bisa laifin sata a coci

Wasu maza 2 zasu bakunci gidan yari na watanni 6 bisa laifin sata a coci

Dukannin barayin ma su shekaru 24, sun amsa laifuka 2 da a ke tuhumar su na zagon kasa da sata. Sun kuma roki kotu ta ma su sassauci, a inda Alkalin kotun, Abubakar sadiq, ya ba wa kowannen su damar biyan tara na N20,000 da gardadi mai zafi a madadin zaman gidan yarin.

KU KARANTA: An gurfanar da wasu a kotu bisa zargin sace kajin wani Sanata

Mai gurfanar da ma su laifin, Dalhatu zanna, ya shaidawa kotun cewar barayin sun aikata laifin satan ne a ranar 2 ga watan Fabrairu da misalin karfe 4:36 na dare, a 'Mountain of Fire Ministry Church' da ke Utako, Abuja.

Sun shiga cocin sun sace wayoyin ne yayin da ma su shi ke bauta. Wani mutumin cocin mai suna Miceal Udikuiri, shi ne ya kai rahoto Ofishin 'Yansanda da ke Utako.

Zanna ya kuma bayyana cewar wadanda a ke zargi da satan sun amsa laifin na su ne yayin da hukuma ke ma su tambayoyi da tuhuma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel