Nigerian news All categories All tags
Satar N21B: Tsohon Janar na neman afuwar gwamnati, yayi alkawarin dawo da kudaden da ya wawashe daga ofishinsa

Satar N21B: Tsohon Janar na neman afuwar gwamnati, yayi alkawarin dawo da kudaden da ya wawashe daga ofishinsa

- Ana tsaka da yakin Boko Haram ya wawure kudaden

- An gano yadda ya dinga canja musu akala da asusu a lokuta da dama, har ya batda sawunsu

- Kadarori ya saya dasu a Ingila

Satar N21B: Tsohon Janar na neman afuwar gwamnati, yayi alkawarin dawo da kudaden da ya wawashe daga ofishinsa

Satar N21B: Tsohon Janar na neman afuwar gwamnati, yayi alkawarin dawo da kudaden da ya wawashe daga ofishinsa

Tsohon Janar na sojin samar Najeriya, wanda tuni yayi ritaya, Chief of Air Staff, Air Marshal Adesola Amosu, ya gaya wa kotu jiya a Legas, cewa yana kan sulhu da gwamnati ta hannun hukumar EFCC da lauyoyinsa, kan yadda zai gujewa shiga kurkuku, da ma dakatar da shari'arsa baki daya.

A cewarsa dai, zasu sami matsaya ne domin ya dawo da kudaden da ya juya wa akala daga Ofishinsa, lokacin yana Janar na sojin sama, daga yaki da Boko Haram zuwa kamfanoninsa.

A baya dai, an bayyana yadda JAnar Amosun, ya kwashe kudaden ya bi dasu ta hanyoyi da dama, inda daga karshe, suka fada asusun kamfanunuwansa, da ma sayen kadarori a kasar Ingila.

DUBA WANNAN: Hukumar raya arewa maso gabas zata fara aiki

Tun bayan hawan gwamnatin nan dai ta Shugaba Buhari, ake ta kara bankado manyan badakala da sata da aka tafka a lokutan baya, daga soji zuwa farar hula, musamman a lokacin da mutane ke tsaka da shan wahalar ta'addanci Boko Haram.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel