Nigerian news All categories All tags
Mutane 200 'yan kungiyar asiri sun tuba, sun mika makamansu ga hukumar 'yan sanda

Mutane 200 'yan kungiyar asiri sun tuba, sun mika makamansu ga hukumar 'yan sanda

- Fiye da mutane 200 'yan kungiyar asiri sun tuba tare da mika makamansu ga jami'an 'yan sandan Najeriya a jihar Legas

- Kwamishinan 'yan sanda a jihar Legas ya bukaci jama'a da su bawa 'yan sanda hadin kai domin yakar aiyukan ta'addanci

- Ya bayyana cewar hukumar 'yan sanda ta dauki bayanan tubabbun 'yan kungiyar asirin domin ci gaba da sa ido a kansu

Fiye da mutane 200 'yan kungiyar asiri sun tuba daga aikata miyagun laifuka tare da mika makamansu ga hukumar 'yan sanda a Ikorodu dake jihar Legas a jiya.

Tubabbun sun mika makamai ga hukumar 'yan sanda da suka hada da bindigun gida 15, adda 11, manyan bindigu 4, gatari 4, kananan bindigun gida 5, takobi guda da kuma alburusai masu yawa.

Mutane 200 'yan kungiyar asiri sun tuba, sun mika makamansu ga hukumar 'yan sanda

Kwamishinan hukumar 'yan sanda na Jihar Legas, Mista Edgar

Da yake jawabi a fadar basaraken da aka karbi tuban 'yan kungiyar asirin, kwamishinan 'yan sanda a jihar Legas, Mista Imohimi Edgar, ya bukaci jama'a da su bawa jami'an 'yan sanda hadin kai domin yakar aiyukan ta'addanci.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Shugabannin hukumomin tsaron Najeriya sun yi gumm da bakinsu bayan ganawa da Buhari

"Akwai wadanda har yanzu basu mika wuya ba, dole ku saka ido don ganin basu ci gaba da aikata miyagun laifuka ba. Jami'an mu zasu hada kai da ku domin murkushe aiyukan ta'addanci a yankin Ikorodu," inji Kwamishina Edgar.

Ya kara da cewar hukumar 'yan sanda zata dauki bayanan tubabbun 'yan kungiyar asirin domin ci gaba da saka idanu a kan mu'amala da motsin su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel