Nigerian news All categories All tags
Shugaba Jacob Zuma na cikin tsaka mai wuya

Shugaba Jacob Zuma na cikin tsaka mai wuya

- Jam'iyyar ANC ta bukaci Jacob Zuma ya sauka daga kan mulki

- Jacob Zuma ya bukaci jam'iyyar ANC ta bar shi akan mukamin sa na tsawon wasu 'yan watanni

Jam’iyyar ANC dake kan mulki a kasar Afrika ta Kudu ta bai wa shugaban kasa, Jacob Zuma wa’adin kwani biyu yayi murabus ko a tsige shi a lokacin da aka gaza samun matsaya a tattaunawar da akayi da shi da ya kwashe tsawon lokaci.

Rahotannin da aka samu daga Kafofin watsa labaru na kasar Afrika ta kudu, sun nuna cewa jam’iyyar ANC za ta aike wa Shugaba Jacob Zuma wasikar sauka daga karagar mulkin kasar bayan ta yi watsi da alfarman da ya nema daga jam’iyyar na cewa a barshi akan mukamin sa na tsawon wasu ‘yan watanni.

Shugaba Jacob Zuma na cikin tsaka mai wuya

Shugaban Kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma

Sai dai har wannan lokaci jam'iyyar ta ANC ba ta sanar da wannan labari a hakumance ba.

KU KARANTA : Mahauta 95 sun kamu da cutar Brucellosis a Bauchi

Amma kuma ta kira wani taron manema labarai Johannesburg.

A shekara 2008 tsohon Shugaba kasar Afrika ta kudu, Mista Thabo Mbeki ya yi murabus daga kan mukamin a lokacin da jam’iyyar ANC ta bukace shi ya sauka.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku ci gaba da bin mu a

Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa

Da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel