Nigerian news All categories All tags
Kotu ta zartar da hukunci a kan 'yan kungiyar Boko Haram 20 dake da hannu a satar 'yan matan Chibok

Kotu ta zartar da hukunci a kan 'yan kungiyar Boko Haram 20 dake da hannu a satar 'yan matan Chibok

- Wata kotun Najeriya ta yankewa 'yan kungiyar Boko Haram 20 hukuncin zaman gidan yari

- Kotun ta ce ta same su da laifukan ta'addanci da satar mutane

- Wannan shine karo na farko da wata kotu a Najeriya ta yankewa wani dan kungiyar Boko Haram hukunci

Wata kotun Najeriya dake zamanta a jihar Neja ta yankewa wasu 'yan kungiyar Boko Haram 20 hukuncin zaman gidan yari.

Wannan shine karo na farko da wata kotun Najeriya ta taba yanke hukunci a kan wani dan Boko Haram dake da hannu a satar 'yan matan Chibok.

Kotu ta zartar da hukunci a kan 'yan kungiyar Boko Haram 20

Wasu daga cikin 'yan matan Chibok

Kotun ta ce ta samu 'yan kungiyar da aikata laifukan kisa, ta'addanci, da kuma satar mutane.

Wani nakasashshe daga cikin wadanda aka zartarwa da hukunci zai shafe tsawon shekaru 15 a kurkuku yayin da ta sallami wasu mutane biyu saboda rashin gamsashshiyar a kansu.

DUBA WANNAN: Hukumar EFCC ta shiga maganar batan miliyan N36m da 'wai' maciji ya hadiye

Wata majiya ta tabbatar wa da Legit.ng cewar kimanin 'yan Boko Haram 700 ake saka ran za'a yiwa shari'a a kotuna hudu cikin satinnan.

Hukumomi sun ce akwai kimanin mutane fiye da dubu a tsare bisa zarginsu da zama 'yan kungiyar Boko Haram.

A watan Oktoba na shekarar da ta gabata an yankewa wasu mutane 45 da aka samu da laifin zama 'yan kungiyar hukuncin daurin shekaru uku zuwa 31 a gidan yari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel