Nigerian news All categories All tags
Yanzu-yanzu: Makiyaya sun kai hari jihar Ondo, sun kori ma'aikata a sakatariyar Akure ta kudu

Yanzu-yanzu: Makiyaya sun kai hari jihar Ondo, sun kori ma'aikata a sakatariyar Akure ta kudu

Rahotanni da Legit.ng ke samu yanzu-yanzun nan na nuni da cewar wasu 'yan ta'adda da ake zargin makiyaya ne sun kai wani hari Ondo tare da korar ma'aikata a sakatariyar karamar hukumar Akure ta a kudu.

Harin makiyayan na zuwa cikin kasa da wata guda da gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akederelu, ke bayyana cewar idan sulhu ya ki aiki za suyi amfani da karfi domin murkushe masu aikin ta'addanci da sunan makiyaya.

Yanzu-yanzu: Makiyaya sun kai hari jihar Ondo, sun kori ma'aikata a sakatariyar Akure ta kudu

Yanzu-yanzu: Makiyaya sun kai hari jihar Ondo, sun kori ma'aikata a sakatariyar Akure ta kudu

Rahotanni sun bayyana cewar yayin harin na safiyar yau, makiyayan sun jiwa wani ma'aikaci a sakatariyar karamar hukumar Akure ciwo bayan da suka sassare shi da adda.

DUBA WANNAN: 2019: Zan samar wa Buhari kuri’u miliyan biyar a Kano – Ganduje

Kwamishinan 'yan sanda a jihar, Mista Gbenga Adeyanju, da shugaban hukumar NCSDC, Mista Pedro Ideba, sun tura jami'ansu wurin ba tare da wani jinkiri ba bayan samun rahoton kai harin. Jami'an sun kwantar da rikicin a halin yanzu.

Ya zuwa yanzu ma'aikata sun tsere dga sakatariyar saboda firgitar da suka yi da harin da makiyayan suka kawo

Zamu kawo maku karin bayani

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel