Nigerian news All categories All tags
Kunnen Patience Jonathan ya yi Laushi, ta nemi sulhu da hukumar EFCC

Kunnen Patience Jonathan ya yi Laushi, ta nemi sulhu da hukumar EFCC

- Uwargidan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ta nemi ayi sulhu a cikin sirri kan tuhumar da EFCC ke mata a kotu

- Ana da tuhumar Patience Jonathan ne dai laifufika da suka shafi mallakan kadarori ba bisa kan ka'ida ba da kuma mallakar kudaden da ba'a san inda suka fito ba da sauransu

- Wata majiya a Hukumar ta EFCC ta ce hukumar na nazarin wasikar kana daga baya zata bayyana amincewa da sulhun ko kuma cigaba da shari'ah a kotu

Bisa ga dukkan alamu uwargidan tsohon shuguban kasa Goodluck Jonathan, Misis Patience Jonathan ta fara ganin ba za ta kai labari ba a shari'ar ta ta dade tana gwabza wa da hukumar yaki da masu wa dukiyar kasa ta'annti, EFCC, hakan yasa ta nemi a yi sulhu a sirrance.

Kunnen Patience Jonathan ya yi Laushi, ta nemi sulhu da hukumar EFCC

Kunnen Patience Jonathan ya yi Laushi, ta nemi sulhu da hukumar EFCC

A wasikar da ta lauyan ta Ifedayo Adedipe ya aike wa hukumar ta EFCC, a ranar 30 ga watan Janairun 2018, Misis Ibifaka Patience Jonathan ta bayyana wa EFCC niyyar ta na yin sulhu a cikin sirri.

KU KARANTA: Zaben 2019: Ka koma gida ka hutu, Junaid ya fadawa shugaba Buhari

A cikin wasikar, Patience ta bayyana bukatar ta na samun lokaci domin zaman tattaunawa da hukumar bisa dukkan zargin da ake mata da kuma iyalan ta. Ta kuma yi alkawarin bada hadin kai yadda ya kamata domin a cinwa matsayaya kyayawa.

Wasikar dai ya zo ne bayan hukumar ta EFCC ta bankado wasu muhimman bayyanai kan yadda Patience ta tara kudade cikin asusun ajiyar ta na banukunan Skye Bank da First Bank.

A cewar jaridar The Nation, Uwargidan tsohon shugaban kasar ta kashe dimbin kudade a wasu biranen duniya da suka hada da kasar Amurka, Jamus, Ingila, China, Italy da sauran su.

Wata majiya daga hukumar ta EFCC ta ce hukumar na nazarin kan wasikar da Patience ta aike don ganin idan za su amince da zaman sulhun ko kuma cigaba da shari'ah a Kotu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel