Nigerian news All categories All tags
2019: Zan samar wa Buhari kuri’u miliyan biyar a Kano – Ganduje

2019: Zan samar wa Buhari kuri’u miliyan biyar a Kano – Ganduje

- Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce shugaba Buhari zai samu kuri’u fiye da miliyan biyar a zaben 2019

- Gwamnan ya bayyana haka ne a yammacin jiya yayin rantsar da sabbin zababbun shugabannin kananan hukumomin jihar

- Ganduje ya ce kuri’un da aka kada yayin zaben kananan hukumomin da aka gudanar ranar Asabar sun zarce adadin kuri’un da Buhari ya samu a 2015

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce shugaba Buhari zai samu kuri’u fiye da miliyan biyar a jihar matukar ya tsaya takara a zaben 2019.

Ganduje ya bayyana hakan ne a yammacin jiya yayin bikin rantsar da sabbin shugabannin kananan hukumomi 44 da kansiloli 484 da aka gudanar da zaben su ranar Asabar ta karshen makon jiya.

2019: Zan samar wa Buhari kuri’u miliyan biyar a Kano – Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje

Kuri’un da aka kada a zaben kananan hukumomi na ranar Asabar sun zarce adadin kuri’un da shugaba Buhari ya samu a zaben 2015. Wannan wata manuniya ce ta karbuwar da jam’iyyar APC ta samu a wurin mutanen jihar Kano da ma kasa baki daya,” inji gwamna Ganduje.

DUBA WANNAN: Sulhunta magoya bayan jam'iyyar APC: An bar gini tun ranar zane, inji wani jigo a jam'iyyar APC

Gwamnan ya kara da cewa “Za mu zazzagawa shugaba Buhari kuri’u a zaben 2019 matukar ya amince ya tsaya takara. Jam’iyyar APC a Kano za ta bayar da gagarumar gudunmawa kamar yadda ta saba.”

Da ya juya kan zababbun shugabannin kananan hukumomi da kansiloli, gwamna Ganduje ya bukace su da su gudanar da mulkinsu bisa gaskiya da rikon amana tare da tabbatar masu da cewar ba zai raga wa duk shugaban da aka samu da laifin almundahana da dukiyar jama’a ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel