Nigerian news All categories All tags
An gurfanar da wasu a kotu bisa zargin sace kajin wani Sanata

An gurfanar da wasu a kotu bisa zargin sace kajin wani Sanata

- An gurafanar da wasu dattawa biyu gaban kotu bisa zargin su da satan kaji guda 6

- Kajin dai mallakin wata gidan gona ce na wani tsohon dan majalisa ne, Sanata Olu Alabi wanda ya wakilci wani yanki daga jihar Osun

- Dattawan biyu da ake tuhuma sun musanta aikata laifin, Kotu ta bayuar da belin su kuma ta dage sauraron karar zuwa 1 ga watan Mayun 2018

An gurfanar da wasu dattawa biyu, Adegoke Atanda dan shekara 65 da kuma Obe Adegbola dan shekatu 50 gaban wata kotun majistare da Osobgo bisa zargin satan kajin gona 6 da kudin su ya kai N9,600.

An gurfanar da wasu a kotu bisa sace kajin wani Sanata

An gurfanar da wasu a kotu bisa sace kajin wani Sanata

Mai shigar da karar, Mista Gafari Muslimi, ya fadawa wa Alkalin kotun, Misis Fartimoh Sodamade cewa wandanda ake zargi sun sace kajin ne daga gidan gonar Olu Alabi da ke Oke-Onitea na Osogbo misalin karfe 10 na daren ranar 10 ga watan Fabrairu.

KU KARANTA: Kunnen Patience Jonathan ya yi Laushi, ta nemi sulhu da hukumar EFCC

Gidan gonar mallakar Sanata Olu Alabi ne wanda ya wakilci yankin Osun ta tsakiya a tsakanin 1991 - 1992. Haka zalika, ya shugabanci hukumar gine-gine na birnin tarayya Abuja.

Sai dai bayan an karanta karar, dattawa biyun sun musanta zargin da ake musu sannan lauya mai kare su, Mista Okobe Najite ya nemi kotu ta bayar da belin su.

Allakin kotun ta amsa rokon sa inda ta bayar da belin su kan kudi N20,000 kowanen su tare da mutum daya da zai tsaya musu.

Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 1 da watan Mayun 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel