Cikin Hotuna: Dangin shugaban hafsin sojin kasa na Najeriya
Legit.ng ta kawo muku hotunan shugaban hafsin sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, tare da 'yan uwan sa, mahaifiyar sa da kuma mahaifin sa; marigayi Alhaji Yusuf Buratai da ya riga mu gidan gaksiya a safiyar yau Juma'a.
Rahotanni sun bayyana cewa, yana daya daga tsaffin soji na kasar nan, wato mazan jiya da suka fafata gumurzu a yakin duniya na biyu.
KARANTA KUMA: Hotuna: Jana'izar mahaifin Buratai
Tuni aka gudanar da jana'izar sa a birnin Maiduguri, kuma aka raki gawar sa har makwancin ta.
Allah ya jikan sa da rahama kuma ya kyauta namu karshen.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng