Da dumi-dumi: Gwamnan jihar Plateau ya sallami dukkan kwamishanonin jihar
Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong, ya sallami dukkan kwamishanonin jihar gaba daya.
Jawabin diraktan yada labaran jihar, Emmanuel Nanle, ya bayyana hakan ne ranan yau Alhamis inda ya umurci dukkan kwamishanonin su sauka daga kujerunsu da gaggawa.
Gwamnan bai bada wani takamamman dalilin sallaman kwamishanonin da ya nada shekaru 2 da suka wucw ba.
KU KARANTA: An ba Sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram kyautar motoci
Jawabin yace: “Gwamnan ya mika godiyarsa ga kwamishanonin bisa ga kokarinsu wajen aiki wa mutanen jihar Flato.”
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng