Majalisar dinkin duniya ta aiko babura da wayoyin salula don ayi mata wasu ayyuka dasu

Majalisar dinkin duniya ta aiko babura da wayoyin salula don ayi mata wasu ayyuka dasu

- WHO ta aiko kayan aiki ne saboda aikin allurai na riga-kafi

- Miliyoyin kudi ta kashe saboda samar da su

- Jihar Kano ta karbi baburan 72 da ma wayoyi 45

Majalisar dinkin duniya ta aiko babura da wayoyin salula don ayi mata wasu ayyuka dasu

Majalisar dinkin duniya ta aiko babura da wayoyin salula don ayi mata wasu ayyuka dasu

WHO, ma'aikatar kiwon lafiya ta majalisar dinkin duniya, ta mikawa gwamnatin jihar Kano babura 72 da wayoyin salula 45 domin aikin kiwon lafiya da ke gudana a jihar.

Ana aikin rigakafin allurai, da ma kula da bullar cuta a kauyukan kananan hukumomi a ffadin kasar nan.

Cutuka irinsu Zika, da Yalo ffifa, da malaria, da Polio da ma su sankarau, duk sune ake aikin kare bullarsu, musamman a yankunan karkara, inda gwamnati bata iya kaiwa cikin kankanin lokaci.

DUBA WANNAN: Ya saki matarsa ya auro 'yar-tsana

Dr. Wondimagegnehu Alemu shine shugaban hukumar a Najeriya, ya kuma mika kayan aikin ga gwamnan jihar Abdullahi Ganduje, domin a habaka aikin kula da kiwon lafiya da kare yaduwar cutuka a karkara.

Gwamnan kuma ya karba, sannan yayi godiya ga hukumar kan kokarinta na kula da kariya da riga-kafi ga kananan hukomin jihar,

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel