Nigerian news All categories All tags
Jam'iyyar APC tayi wa jam'iyyar adawa ta PDP zigidir a jihar Osun

Jam'iyyar APC tayi wa jam'iyyar adawa ta PDP zigidir a jihar Osun

Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Osun watau Osun Independent Electoral Commission a turance ta sanar da cewa jam'iyya mai mulki a jihar ta APC ta yi nasarar lashe dukkanin kujerun kansilolin jihar a zaben da aka gudanar a karshen satin da ya gabata.

Da ya ke ayyana sakamakon zaben, shugaban hukumar zaben ta Osun Independent Electoral Commission mai suna Mista Segun Oladitan ya bayyana cewa mutane 318 daga cikin su an sake zaben su ne ba hamayya.

Jam'iyyar APC tayi wa jam'iyyar adawa ta PDP zigidir a jihar Osun

Jam'iyyar APC tayi wa jam'iyyar adawa ta PDP zigidir a jihar Osun

KU KARANTA: Jam'iyyar adawa a Kano za ta san matsayin ta gobe

Legit.ng ta samu haka zalika cewa tuni dai har hukumar ta bayar da shaidar cin zaben hukumar zuwa ga kansilolin jim kadan bayan kammala sanarwar.

A wani labarin kuma, Wani kwararren dan siyasa kuma shugaban wata kungiya mai rajin kare muradun shugaba Muhammadu Buhari ya shawarci shugaban da ya kalli wasikar Obasanjo zuwa gareshi a matsayin wata hanya za ta taimaka masa waen lashe zaben sa na 2019.

Shugaban kungiyar dai na kasa watau National Coordinator for Buhari Solidarity Movement, Ovo Ofigo, shine ya sanar da hakan a cikin wata sanarwar da ya rabawa manema labarai a karshen satin da ya gabata.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel