Nigerian news All categories All tags
Dakarun soji sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram bakwai

Dakarun soji sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram bakwai

- Dakarun rundunar Ofireshon Lafiya Dole sun yi kwanton bauna ga wasu mayakan kungiyar Boko Haram

- Kukasheka, kakakin rundunar soji, ya ce, hukumar soji na cigaba da kakkabe ragowar mayakan kungiyar a fadin jihar Borno

- Ya ce dakarun sojin sun kashe mayakan kungiyar ne a ranar Juma'a

Dakarun rundunar Ofireshon Lafiya Dole mai aikin tabbatar da zama lafiya a jihar Borno ta yiwa mayakan kungiyar Boko Haram kwanton bauna tare da kashe mutane bakwai daga cikinsu bayan ta tarwatsa tawagar su yayin da su ke kokarin guduwa zuwa dajin sambisa.

Dakarun soji sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram bakwai

Dakarun sojin Najeriya

Kakakin rundunar soji ta kasa, Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka, ya sanar da hakan a wani jawabi ga manema labarai ranar Asabar. Ya ce hukumar sojin Najeriya na cigaba da share ragowar mayakan kungiyar Boko Haram a karkashin aikin rundunar hukumar da ta saka wa suna "Ofireshon naushi mai nauyi II" domin ragargazar ragowar mayakan kungiyar Boko Haram dake dajin Sambisa da ma ragowar sassan jihar.

DUBA WANNAN: An yi tankade da rairaya a hukumar sojin sama ta kasa

"A ranar Juma'a ne, rundunar mu ta sojin kasa tare da hadin gwuiwar wata rundunar sojin sama, ta kai farmaki kan wata tawagar mayakan kungiyar Boko Haram yayin da suke hanyar su ta zuwa dajin Sambisa. Rundunar mu ta yi nasarar fasa tawagar tare da kashe mayakan kungiyar su bakwai," inji Kukasheka.

Kukasheka ya kara da cewar rundunar sojin ta yi nasarar kama wasu makaman mayakan kungiyar bayan da su ka gudu yayin da suka sha wuta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel