Nigerian news All categories All tags
Karancin man fetur : Hukumar FRSC ta yi gargadi akan daukar man fetur a cikin motoci

Karancin man fetur : Hukumar FRSC ta yi gargadi akan daukar man fetur a cikin motoci

- Hukumar FRSC ta ce daukar man fetur a cikin mota yana da matuka hatsari

- FRSC ta yi kira direbobi suyi hakuri su bi doka har gwamnati ta samu nasar kawo karshen karancin man fetur a kasar

Hukumar kula da matafiya da lafiyar hanyoyi (FRSC) ta gargadi matafiya akan daukar man fetur a cikin motocin su, saboda kauracewa wahalar mai a lokacin da suka yi tafiya.

Shugaban hukumar FRSC reshen jihar Ogun yayi wannan gargadi a lokacin da yake zantawa da manema labaru a ranar Lahadi a Ogun.

Karancin man fetur : Hukumar FRSC ta yi gargadi akan daukar man fetur a cikin motoci

Karancin man fetur : Hukumar FRSC ta yi gargadi akan daukar man fetur a cikin motoci

Oladele ya ce hukumar FRSC ta yi wannan gargadi ne saboda kare rayuka dukiyoyi daga gobara ta sanadiyar yawo da man fetur a cikin mota.

KU KARANTA : Rikicin siyasar Kano: Zamu kwace kujeran Kwankwaso a 2019 - Ganduje

Daukan man fetur a cikin mota ya na da matukar hatsari, saboda idan gobara ya tashi zai hadda mutanen dake nesa.

Oladele ya ce, hukumar FRSC ta kama jarkoki cike da man fetur a cikin motocin da suka tsare.

Yayi kira da direbobin dake daukan man fetur a cikin motocin su, da suyi hakuri su bi doka har gwamnati ta shawo kan matsalar karancin man fetur a kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel