Nigerian news All categories All tags
Miliyoyin 'yan Najeriya zasu dawo APC kwanan nan - Alhaji Muhammadu Buhari

Miliyoyin 'yan Najeriya zasu dawo APC kwanan nan - Alhaji Muhammadu Buhari

- A wasikar da ya aike wa Sanata Bashir Muhammed ya fadi hakan

- Sanatan ya jawo zugarsa ya zuwa APC a makon nan

- Buhari zai iya neman takara a karo na biyu a badi a APC

Miliyoyin 'yan Najeriya zasu dawo APC kwanan nan - Alhaji Muhammadu Buhari

Miliyoyin 'yan Najeriya zasu dawo APC kwanan nan - Alhaji Muhammadu Buhari

A wasika da ya aike wa Satana na Kano, Bashir Muhammed, wanda ya dawo APC a makon jiya, ta taya shi murnar hawowa tudun-mun-tsira, Shugaba Buhari ya ce ai ba Sanatan kadai ba, yana sa rai har sauran 'yan Najeriya zasu shigo APC cikin watannin nan.

Shugaban dai ya ce a cikin wasikar, wadda kafafen yada labaru suka sami kwape, cewa miliyoyin mutane na kasar nan ne zasu dinga rajista da APC a watanni masu zuwa, sannan ya taya sanatan da jama'arsa murna.

DUBA WANNAN: Kotu ta dakatar da kisan wani ba'amurke da ya manta laifinsa

Ana sa rai dai kafin a kai ga karshen shekarar nan, shugaba Buhari zai fadi aniyarsa ta tsaya wa takara a zango na biyu, muddin dai lafiyarsa ta ci gaba da kyautata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel