Nigerian news All categories All tags
Wani Ma’aikacin kwastan na bogi a wata kasa ya shiga hannu

Wani Ma’aikacin kwastan na bogi a wata kasa ya shiga hannu

- An kama wani Jami’in Kwastam na karya a Kasar Kwadebuwa

- Wannan mutum ya dade yana wannan aikin na bogi a cikin kasar

- Sai kwanan nan dubun sa ta cika Hukuma tayi ram da shi a hannu

Kwanan nan mu ka samu wani labari mai cike da ban mamaki inda aka yi ram da Ma’aikacin kwastan da yayi shekaru aru-aru yana aiki amma na bogi a wata kasar a nan cikin gida Afrika ba a gane ba.

Wani Ma’aikacin kwastan na bogi a wata kasa ya shiga hannu

An kama Ma’aikacin Kwastam na karya a Ibori-kwas

Jaridar Rariya ta kawo rahoton wani mutumi a kasar Kwadebuwa wanda ya dauki shekaru sama da 7 yana aiki a matsayin Jami’in Hukumar kwastam na kasar amma babu wanda yayi iya gane cewa Ma’aikacin karya ne.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ne kadai ba barawo ba a Najeriya – Lauretta Onochie

Wani Ma’aikacin kwastan na bogi a wata kasa ya shiga hannu

Dubun Ma’aikacin Kwastam din bogi ta cika

Dama dai karshen tika-tika shi ne tik don kuwa wannan mutumi ya shiga hannun Hukumar kasar ta Kwadebuwa. Duk rana ta Allah wannan mutumi ya kan sa khakin sa kamar gaske ya dafe kan iyakokin kasar ta Kwadebuwa.

A kowace rana ta Allah kamar yadda mu ka samu labari wannan Bawan Allah zai dauki ‘yar bindigan sa yayi gaba da sunan ya fita aiki. Sai wannan karo ne aka samu damar damke shi.

Dubu ta cika inda aka kama Ma’aikacin Kwastam na karya Wannan mutumi yayi shekaru da dama yana aikin bogi. Kullum sai ya sagala bindiga ya ci kaya zuwa wurin aiki. Ashe duk wannan shekaru Ma'aikacin karya ne ba a sani ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel