Nigerian news All categories All tags
Kaso 80% na sanatocin arewa na na tare da Obasanjo – Sanatan Arewa

Kaso 80% na sanatocin arewa na na tare da Obasanjo – Sanatan Arewa

- Rahotanni sun tabbatar da cewar wasu ‘yan majalisar dattijai daga arewacin Najeriya na tare da tsohon shugaban kasa Obasanjo

- Sanatocin sun nuna goyon bayansu ga Obasanjo tare da bayyana niyyar su ta binsa sabuwar jam’iyyar da zai shiga ko ya kafa

- Akwai yiwuwar jam’iyyun APC da PDP su yi asarar magoya baya da zarar obasanjo ya bayyana mataki na gaba

Kudirin tsohon shugaban kasa Obasanjo na kafa sabuwar jam’iyya da za ta kawo karshen mulkin jam’iyyar APC a zaben shekarar 2019 na kara samun gindin zama bayan da wasu ‘yan majalisar dattijai su ka bayyana shirinsu na bin sahun Obasanjo duk inda ya saka kafar sa.

Tsohon shugaba Obasanjo dai ya rubuta wata zungureriyar wasika ga shugaba Buhari yana mai shawartar sa da kada ya kuskura ya tsaya takara a zaben shekarar 2019 tare da bayyana bukatar kafa sabuwar jam’iyya da za ta maye gurbin jam’iyyun APC da PDP.

Kaso 80% na sanatocin arewa na na tare da Obasanjo – Sanatan Arewa

Buhari da Obasanjo a Addis-Ababa a yau

Jaridar Punch ta rawaito cewar wani mamba dan jam’iyyar APC daga arewa a majalisar dattijai ya tabbatar ma ta cewar kaso 80% na ‘yan majalisar na tare da Obasanjo. Dan majalisar da bai yarda a bayyana sunansa ba ya ce, akwai tsofi da gwamnoni masu ci da su ka bayyana niyyar su ta shiga cikin sabuwar tafiyar ta Obasanjo.

Da gaske ne Obasanjo ya tuntube mu kuma tabbas muna tare da shi don kuwa kaso 80% cikin dari na 'yan majalisar dattijai daga arewa na goyon bayansa. Muna da yawa, mu ne keda rinjaye ma. Yi wa sabuwar jam’iyya rijista ba zai dauki sama da sati biyu ba. Kuma a halin yanzu ma akwai jam’iyyar da muke saka ran dauka,” a cewar sanatan.

DUBA WANNAN: Hotunan Gwamna da jami'an gwamnatinsa yayin atisaye a kan Kekuna

Ina mai tabbatar maku cewar daga wata mai kamawa zaku fara samun labaran canjin sheka ya zuwa sabuwar jam’iyyar mu,” inji sanatan.

Sannan ya kara da cewar akwai ‘yan majalisar daga jam’iyyun APC da PDP da basa jin dadin jam’iyyunsu da kuma yadda al’amuran gwamnatin Buhari ke tafiya tare da bayyana cewar jam’iyyar APC kan iya komawa marar rinjaye a zauren majalisar domin da yawan mambobin majalisar ba zasu samu tikitin kara yin takara a jam’iyyar ba a jihohinsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel