Nigerian news All categories All tags
Gwamnati ta yi karin haske kan cece-kuce da nadin shugaban NIA Abubakar ya jawo

Gwamnati ta yi karin haske kan cece-kuce da nadin shugaban NIA Abubakar ya jawo

- Adesina ya karyata cewa Abubakardin ba dan Najeriya bane

- Ya kuma ce labarin wai yana auren 'yar Morocco ba gaskiya bane

- Ya kuma karyata wai DG ya fadi jarrawabar karin matsayi

Gwamnati ta yi karin haske kan cece-kuce da nadin shugaban NIA Abubakar ya jawo

Gwamnati ta yi karin haske kan cece-kuce da nadin shugaban NIA Abubakar ya jawo

Kakakin shugaba Buhari, Femi Adesina, kuma hadiminsa kan yada labarai, ya saki bayanai kan sabon shugaban hukumar leken asiri ta kasa watau NIA, Malam Ahmed Rufai Abubaka, inda yace lokaci yayi da za'a bayyana waye shi.

A cewar Adesina a shafin sa na facebook, yace tunda yanzu Abubakar ya hau matsayin shugaban dole ne kuma mu fayyacewa 'yan Najeriya ko shi waye, mu kuma karyata labaru da ake ta yayatawa a shafukan sada zumunta da ma kafofin yada labarai.

DUBA WANNAN: In Buhari ya dage zamu yaga APC

Ya bayyana dattijon a matsayin mutum mai hazaka wanda ya iya aikinnsa, kuma Buhari ya yarda da shi. Yace batun wai bai kai matsayin darakta ba, yace a mataimakin darakta ya ajje aiki, haka kuma karya ne wai bai ci jarrabawarr karin matsayi ba.

Ya kuma karyata cewa wai Malam Abubakar din dan Chadi ne ko kuma yna auren 'yan Morocco, inda yace, duk wannan karairayi ne.

Ya ce kafin a yayata karya, ya kamata a rinka tantancewa domin gudun abin kunya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel