Nigerian news All categories All tags
2019: Barayin PDP ke hada kai don kifar da mu - Lai Mohammed

2019: Barayin PDP ke hada kai don kifar da mu - Lai Mohammed

- Barayin PDP sun hada kai don yakar adalci inji kakakin gwamnati

- Wasikar Oasanjo ta tayar wa da 'yan APC hankali

- Ana gab da zabukan 2019, kuma masu mulki basu son juyi

2019: Barayin PDP ke hada kai don kiar da mu - Lai Mohammed

2019: Barayin PDP ke hada kai don kiar da mu - Lai Mohammed

Kakakin gwamnati kuma ministan yada labarai da al'adun Najeriya, Alhaji Lai Muhammed, ya soki jam'iyyun adawa da kushe su a matsayingaggan barayi masu son su kifar da gwamnati ta APC wadda ya kira mai adalci.

A zantawarsa da manema labarai, martanin wasikar Obasanjo, dattijon, yace taron dangi ake kokarin a yi wa wannan gwamnati tasu a kore su daga ffadar gwamnati, domin a ci gaba daga inda aka tsaya ta almundahana da sata.

DUBA WANNAN: In Buhari ya dage zamu yaga APC

Mulkin Buhari dai, an ja kafa sosai, jama'a kumma suna jin jiki, amma kuma an kamo kudaden sata wadanda tsohuwar gwamnati ta yi rabon wasoso da su.

Sai da aka kai ruwa rana, aka kama har da wasu alkalai kan cin hanci da karbar na goro don jan lokaci kan shari'ar da ake yi wa masu sata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel