Nigerian news All categories All tags
Zan maida Jihar Kogi tamkar kasar Turai - Gwamnan da ake bin bashin albashin shekaru

Zan maida Jihar Kogi tamkar kasar Turai - Gwamnan da ake bin bashin albashin shekaru

- Jihar Kogi bata iya ko biyal albashi banda uban bashi da ke kanta

- Gwamna Bello ya ce zai maida jiharsa kamar kasar Netherlands

- A harkar sayar sa nonon shanu da noma gwamnan ke hobbasa

Zan maida Jihar Kogi tamkar kasar Turai - Gwamnan da ake bin bashin albashin shekaru

Zan maida Jihar Kogi tamkar kasar Turai - Gwamnan da ake bin bashin albashin shekaru

Gwamna Bello na jihar Kogi, ya lashi takobin mayar da jiharsa uwar kindirmo a Najeriya, kamar yadda Holland take a duniya. Kasar Holland ita ce kasa da ke samar da madara da kiwo ffiye da kowa a nahiyar turawa.

Gwamnan, wanda jiharsa ke cikin kaka nika yi kan biyan albashi da rashin aikin yi ga samari, ya ce a harkar noma, jiharsa sai ta fi kowa nan gaba kadan, inda zata yi kiwo da sayar da kayan dabbobi, kamar su fata da kofatai don yin gam.

DUBA WANNAN: An yi kira ga shugaba Buhari da ya kawo karshen Almajirci

A hobbasarsa dai, yace zai ware wuraren kiwo da kula da dabbobi na zamani, sannan zai samar da injina da kuma tallafi ga masu sha'awar yin kiwo, musamman na shanu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel