Nigerian news All categories All tags
Yadda Buhari ya rage darajar mulkin sa daga shugaban kasar Najeriya sa zuwa shugaban Katsina - Adebanjo

Yadda Buhari ya rage darajar mulkin sa daga shugaban kasar Najeriya sa zuwa shugaban Katsina - Adebanjo

- Ayo Adebanjo yace sukar gwamnatin Buhari da Obasanjo yayi a budadiyar wasikar da ya rubutawa Buhari gaskiya ne

- Adebanjo ya ce sauya fasalin Najeriya kadai mafita ga matsalolin da kasar fuskanta

Shugaban kungiyar ‘yarbawa na Afenifere, Ayo Adebanjo, ya zargi shugaban kasa, Muhammadu Buhari da rage darajar mulkin sa daga shugaban Najeriya zuwa shugaban kasar katsina.

Adebanjo yayi wannan kalaman ne a lokacin da yake mayar da martani akan sukar gwamnatin Buhari da Obasanjo yayi.

Jagoran kungiyar Afenifere yace, ya kamata Buhari ya fahimce cewa sauya fasalin kasar ne kadai mafita ga matsalolin da kasar ke fuskanta.

Yadda Buhari ya rage darajar mulkin sa zuwa shugaban kasar Katsina - Adebanjo

Yadda Buhari ya rage darajar mulkin sa zuwa shugaban kasar Katsina - Adebanjo

Yace, “Idan Buhari dagaske yake yana son zaman lafiya da hadin kai ‘yan Najeriya, kiran kowa teburi zai yi a zauna a tattauna matsalolin da kasar ke fuskanta, bai wai yayi shiru ya zura idanu yana kallo ana kashe wasu ba tare da yin komai ba. Wannan hali nasa ya mayar da shi shugaban Katsina.

KU KARANTA : Abun kunya ne yadda babu wata matatan man fetur da ke cikakken aiki a Najeriya, inji Shugaba Buhari

Da yake jawabi akan wasikar Obasanjo, Adebanjo ya ce, “Maganar da Obasanjo yayi na cewa jam’iyyar APC da PDP ba za su iya gyara Najeriya ba gaskiya ne.

“Amma duk wani jam’iyya da Obasanjo ya nuna ra’ayin sa akai ba ruwan mu da ita, saboda Obasanjo ba ya goyon bayan abun alheri”.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel